Helkwatar tsaro a Najeriya ta ce ta samu nasarar hallaka yan ta’adda 82 tare da kama wasu masu aikata laifi 198.

Sannan helkwatar ta kuma kubutar da mutane 93 da aka yi garkuwa da su.
Nasarar dai ta sameta ne cikin mako guda.
Daraktan yaɗa labarai na helkwatar Manjo Janar Markus Kangye ne ya bayana haka a wata sanarwa da ya fitar ya Juma’a.

Ya ce akwai wasu yan ta’adda 41 da su ka mika wuya
Daga ciki akwai maza goma, mata 12, da yara 19

Daga yankin Neja Delta kuwa jami’an sun kwato danyen mai da ya kai naira miliyan 500.
Sannan sun kama mutane 22 da ake zargi da satar danyen mai, tare da kwato makamai 152.
Daga ciki akwai bindigu kirar AK47 guda 46 da bindigu kirar gida guda 18 sai manyan bindigu guda 19.