Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Kano SEMA tare da hukumar ta ƙasa NEMA, ta ƙaddamar da rabon kayan tallafi ga magidanta 507 da ambaliyar ruwa ta a shekarar 2024.

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ne ya tabbatar da miƙa kayan tallafin ga waɗanda su ka rabauta, a ƙananan hukumomin Kibiya da Madobi da ke jihar.

Gwamna Abba wanda ya samu wakilcin Kwamishinan jin ƙai da magance fatara Adamu Aliyu Kibiya, ya jinjinawa hukumar ta NEMA bisa ƙoƙarinta na taimakawa da kayan tallafi a jihar.

Ya kuma jinjinawa hukumar ta jiha SEMA bisa jajircewarta na tabbatar da kayan tallafin sun isa ga waɗanda abin ya shafa.
Ya kuma ƙara da cewa gwamnatin jihar Kanon za ta ci gaba da haɗa kai da gwamnatin tarayya da sauran hukumomin jihohi, dan tabbatar da tsaro da walwalar al’umma.
A nasa ɓangaren babban daraktan hukumar ta NEMA a jihar Zubaida Umar ta bayyana cewa, wannan wata karramawar ɓangare ne na gwamnatin tarayya a ƙoƙarinta na tallafawa waɗanda ambaliyar ruwan ta shafa.