Gwamnatin Jihar Yobe ta sanya hannu akan fitar da naira biliyan 22.3, da za a yi amfani dashi wajen ginin gadar sama da titin karkashin Kasa a garin Damaturu babbab birnin Jihar.

Kwamishinan ayyuka na Jihar Injiniya Umar Duddaye ne ya sanya hannun a madadin gwamnatin Jihar, inda kuma Injiniya Habib Geojea ya wakilci Kamfanin Messrs Triacta Nigeria Limited da aka bai’wa kwangilar.

Acewar Kwamishin gwamnatin Jihar karkashin jagorancin gwamna Mai Mala Buni ta himmatu wajen samar da manyan ayyuka a fadin Jihar.

Duddaye ya ce daga cikin ayyukan da gwamnatin Jihar tafi bai’wa fifiko sun hada da samar da tituna, gida gadoji da kuma magudanan ruwa da dai sauransu.

Kwamishinan ya kara da cewa aikin za a kammala shi ne a ciki watannin 12.

Har ila yau Kwamishinan ya kuma bayyana cewa an sake rattaba hannun akan ginin titin Damaturu zuwa Gambir tsakanin gwamnatin Jihar da kamfanin Messrs Elegance Construction Nigeria Limited, kuma za kammala shi a cikin watanni Tara.

Bugu da kari Duddaye ya bayyana cewa gwamnatin Jihar na kuma shirin gina sabbin tituna masu tsawon kilomita 23.5, da gyara titunan da ake bukata, da kuma samar da magudanan ruwa masu nisan kilomita 27 a garin na Damaturu, inda aikin zai kai mataki na biyu a shekarar nan ta 2025.

Ya ce gwamnatin Jihar ta dauki matakin hakan ne domin kara samarwa da al’ummar jihar ababan more rayuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: