Jam’iyya mai mulki a Najeriya APC ta sanya ranakun Talata da Laraba, 26 da 27 ga watan Fabarairu, don gudanar da babban taron masu ruwa da tsakin jam’iyyar na ƙasa.

Sakataren jam’iyyar na ƙasa Sanata Surajudden Bashiru ne ya sanar da hakan, jiya Juma’a a babban birnin tarayya Abuja.
Ta cikin Sanarwar, taron masu ruwa da tsakin jam’iyyar na ƙasa zai gudana ne a ranar Takay, a ɗakin taro na Banquet da ke fadar shugaban ƙasa a birnin tarayya Abuja.

Yayin da ganawar babban kwamitin zartarwa na jam’iyyar zai gudana a ranar Laraba da ƙarfe 10:00 na safe, a sakatariyar jam’iyyar da ke Wuse 2 a birnin na Abuja.

Wata majiya mai tushe daga jam’iyyar ta tabbatar da cewa, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ya amince da ranakun taron.