Rundunar ‘yan sandan Jihar Adamawa ta tabbatar da yin garkuwa da wasu limaman mabiya addinin kirista biyu a Jihar, Rabaran Mathew David Dusami da ke cocin Katolika a garin Yola da kuma Abraham Samman da ke garin Jalingo duk a Jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar CP Dankombo Morris ne ya tabbatar da garkuwa da Limaman na kirista.


Kwamishinan ya ce maharan sun yi garkuwa da su ne da safiya yau Asabar a cikin gidan daya daga cikinsu da ke Gwaida Malam a karamar hukumar Numan ta Jihar.
Dankombo ya ce maharan sun sace su ne da misalin karfe hudu na Asubahin yau, a harin da suka kai garin.
Acewarsa bayan faruwar lamarin tuni suka aike da jami’ansum, bin sahun ‘yan bindigar don kubtar da su.