Akalla mutane 12 suka rasa rayukansu a yayin wani hadarin mota da ya afku akan hanyar Lapai zuwa Agaie a Jihar Neja.
Hadarin da ya faru a yau Asabar ya rutsa da maza Takwas Mata Hudu.
Wani shaidan gani da ido ya shaidawa Jaridar Daily Trust cewa mata uku daga cikin wadanda hadarin ya rutsa da su ‘yan gida guda ne.
A yayin hadarin direban motar da wasu fasinjoji mata biyu sun tsallake rijiya da baya, inda aka mika su ga Babban Asibitin garin Lapai.
Rahotannin sun bayyana cewa hadarin ya faru ne bayan wata arangama da motar ta yi da wata mota Kirar bas mai dauke da fasinjoji 15 tare da wata tirela a daidai Kauyen Nami a Jihar.
Kwamandan Hukumar Kiyaye afkuwar Hadurra FRSC ta Jihar Kumar Tsukwam ya tabbatar da faruwar lamarin.
Hukumar kiyaye afkuwar haddura ta kasa reshen Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane 17 uku su ka jikkata a wani hadarin mota da ya afku a kauyen Yaura da ke kan titin Wudil zuwa Bauchi da ke karamar hukumar Albasu a Kano. Kwamandan hukumar Ibrahim Sallau Abdullahi ne ya…
Hukumar kiyaye afkuwar haɗurra ta ƙasa FRSC ta bayyana cewa, mutane 23 ne suka rasa rayukansu a wani haɗarin mota da ya afku ranar Alhamis, a gadar sama ta Muhammadu Buhari da ke Hotoro a Kano. Ta kuma sanar da cewa, akwai ƙarin mutane 48 da su ka samu…
Hukumar kiyaye afkuwar hadurra ta kasa reshen Jihar Neja ta tabbatar da faruwar wani hadarin babbar mota da ya afku a Jihar, wanda yayi sanadiyyar rasa rayukan mutane 17 da dama kuma suka jikkata. Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Laraba a…