Jam’iyyar PDP da ke mulkin jihar Osun, ta lashe zaben dukkanin kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 30 da kansilolinsu 332 da aka gudanar a jihar jiya Asabar.

Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar OSSIEC Hashim Abioye, shi ne ya sanar da sakamakon zaben a gidan talabijin mallakin jihar da ke Osogbo.
Abioye ya bayyana cewa kimanin jam’iyyun siyasa 18 su ka shiga zaɓen da aka gudanar, kuma sakamakon aka aike da shi zuwa shalkwatar hukumar.

Ya kuma bayyana cewa an gudanar da zaɓen cikin nasara, bisa tsarin doka da sharuɗan da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar, kuma an yi zaɓen ne don cike guraben kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 30 da kansilolinsu 332.

Hashim ya kuma numi afuwar kafafen yada labarai, bisa gazawar hukumar zaɓe wajen bayar shaidar tantancewa ga aikin ɗaukar rahoton yadda zaɓen ya gudana.
Inda ya yi zargin cewa jami’an tsaro ne su ka kulle ofishin hukumar, wurin da kayayyakin su ke a ajiye.
Sai dai kafin a kai ga bayyana sakamakon zaben, tuni babbar jam’iyyar hamayya a jihar ta APC ta ayyana ficewarta daga shiga zaben da aka gudanar, cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar APC a jihar Alao Kamoru ya fitar.