Ƙungiyar malaman Jami’o’i ta ƙasa ASUU reshen jami’ar jihar Kaduna, ta dakatar da yajin aikin da ta tsunduma tun a ranar 18 ga watan Fabarairun nan da mu ke ciki.

Wannan na ƙunshe ne cikin wani jawabi da shugaban ƙungiyar ta ASUU reshen jami’ar Dakta Peter Adamu, ya fitar ga manema labarai a yau Litinin.

Adamu ya bayyana cewa sun yanke shawarar janye yajin aikin da su ke yi ne, tun a ranar Asabar ɗin ƙarshen makon da ya gabata.

Ya ce gwamnatin jihar ta yi shirin magance matsalar, ta hanyar sakin kuɗi nan take don fara biyansu kashi 60 cikin 100 na kuɗin albashin da aka riƙe musu na watan Satumbar shekarar 2017, da kuma alawus ɗin zuwa duba ɗalibai da su ke koyon sanin makamar aiki na zangunan karatu guda biyar.

Ya ƙara da cewa gwamnatin kuma ta amince da biyan albashi na tsawon watanni biyar daga watan Mayu zuwa Satumbar shekarar 2022 da aka riƙe musu, da kuma sauran kuɗaɗe da su ke bi na ɓangarori daban-daban aƙalla guda biyar.

Ƙungiyar ta nuna godiyarta a gwamnan jihar Uba Sani bisa saurin shigarsa cikin batun, tare da kuma bayyana cewa gwamnatin ta nuna da gaske ta ke wajen tabbatar da tsarin biyan albashin, da kuma bayar da ƴancin cin gashin kai ga jami’ar.

A ƙarshe kungiyar ta godewa shugabancin hukumar jami’ar da Kwamishinan ilimi da ma dukkan sauran masu ruwa da tsaki, tare da umartar ƴaƴan ƙungiyar da su koma bakin aiki dan ci gaba daga inda su ka tsaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: