Babbar jami’ar asusun tallafawa yara na majalisar dinkin duniya UNICEF a jihar Bauchi Dakta Nuzhat Rafique ta bayyana cewa, jihar ta Bauchi ce ke kan gaba wajen yawan yaran da ba sa samu abinci mai gina jiki da su ka kai aƙalla guda dubu 54.

Ta bayyana hakan ne yayin wani taron wayar da kai da ya gudana a birnin Jos ɗin jihar Filato, bisa ƙudurin zaburar da shugabannin ƙananan hukumomi a jihar Bauchi da su bunƙasa tsarin kashe kuɗi a ɓangaren cimakar ƙananan yara da kuma walwalarsu.
Rafique ta kuma bayyana damuwarta dangane da adadin yawan yaran da ba sa samun abincin mai gina jiki a matakan ƙananan hukumomi, musamman a asibitocin sha-ka-tafi.

Inda ta ce aƙalla yara uku ne daga cikin kowanne 10 su ke fama da tsananin ƙarancin abinci a jihar Bauchi, inda shida kuma cikin 10 su ke matakin tsaka-tsaki, kuma su ma su na kan gaɓar faɗawa gurbin waɗancan na farkon a kowanne lokaci.

Ta kuma ƙara da cewa ƙananan hukumomi aƙalla 13 daga cikin ƙananan hukumomin jihar, su na da yaran da basu taɓa ko zuwa karɓar allurar rigakafi ba.
Sai dai ta yabawa gwamnatin jihar musamman Gwamna Bala Muhammad da shugabannin ƙananan hukumomin bisa ƙoƙarin da su ke yi, tare da kira da sauran al’umma cewa su ma su na gagarumar rawar takawa dan shawo kan matsalar.
Da ya ke jawabi a wajen taron shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi ta jihar kuma shugaban ƙaramar hukumar Bauchi Mahmoud Babamaji, ya gamsu da ƙalubalen tare da aniyar tabbatar da yin rigakafin a yankunan da ke jihar.