Shugaban rukunonin kamfanin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa, yanzu haka matatar man fetur ta Dangote tana da ajiyayyen man fetur aƙalla lita miliyan 500 a ma’adanarta.

Ya kuma ƙara da cewa matatar tana samar da isashshen man fetur da zai wadaci cikin ƙasa Najeriya har ma da wanda za a fitar zuwa ƙasashen ƙetare.
Dangote ya yi wannan maganar ce dai a ƙarshen makon da ya gabata yayin wani rangadi a matatar man da ke Lekkin jihar Legas, tare da Ministan makamashi na ƙasar Zambiya Makozo Chikote.

Ministan dai ya ziyarci matatar man fetur ta Dangote da ke Legas ne, don buƙatar haɗin guiwa da mamallakinta wajen magance matsalar makamashi da ƙasar ke fama da ita.

Da ya ke ci gaba da jawabi yayin rangadin Dangote ya ƙara da cewa yanzu haka matatar tana ajiye da kaya na aƙalla Naira miliyan dubu 600, kuma za ta kai ga cin samar da ganga dubu 650 a kullum nan da wata mai kamawa, kuma ƙasa Najeriya ba za ta iya shanye kashi 50 cikin 100 na man da su ke samarwa ba.
Da ya ke jawabi game da ingancin man Dangote ya ce, yanzu haka ana rufe matatun mai da yawa a ƙasashen duniya saboda matatar man ta su, tare da cewa babu wata matatar mai a duniya da za ta iya samar da ingantaccen man da su ke samarwa.
Ya kuma ƙara da cewa yanzu haka ƙasa Najeriya na iya shan kashi 40 ne kawai na man da su ke samarwa, inda kashi 60 ɗin kuma ake fita da shi zuwa ƙasashen ƙetare musamman na nahiyar Afirka.