Jam’iyyar APC ta yi Allah wadai tare da yin watsi da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi da aka gudanar ranar Asabar din da ta gabata a jihar Osun, ƙarƙashin jagorancin gwamna Ademola Adeleke na jihar da jam’iyyarsa ta PDP.

Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa Felix Morka ne ya bayyana hakan jiya Lahadi a birnin tarayya Abuja, inda ya bayyana zaɓen a matsayin haramtacce da kuma bijirewa umarnin kotu.
Ya bayyana cewa kotun ɗaukaka ƙara ranar 10 ga watan Fabarairu ta tabbatar da dawo da tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomin jihar da Adeleke ya sauke, hukuncin da ya warware umarnin babbar kotun tarayya na ranar 22 ga watan Nuwamban shekarar 2022.

Morka ya ƙara da cewa hukuncin kotun ɗaukaka ƙara tuni ya warware umarnin kotun baya, tare da tabbatar da shugabannin ƙananan hukumomin akan kujerunsu har zuwa ƙarshen zangon mulkinsu a watan Oktoban shekarar nan ta 2025.

Ya kuma soki tsarin na gwamna Adeleke wanda ya naɗa kantomomin riƙo da cewa ya saɓa da sashi na 7(1) na kundin tsarin mulkin Najeriya, tare da bayyana cewa jam’iyyarsu ta APC tana girmama hukuncin kotu.
A ƙarshe Felix ya yi kira da jami’an tsaro da su sanya ido dan tabbatar da zaman lafiya, tare da kira ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar da cewa halastattun shugabannin ƙananan hukumomi da kotu ta yarda da su ne za a bai’wa kuɗaɗen ƙananan hukumomi.