Rundunar sojin Najeriya ta ce nan bada jimawa ba za ta kawo karshen hatsabibin dan bindigar nan Bello Turji.

Babban daraktan ayyuka na hedkwatar tsaro ta Kasa Manjo Janar Emeka Onumajuru ne ya tabbatar da hakan a yau Litinin ta cikin shirin ‘The Morning Brief’ na gidan Talabijin na Channels.
Emeka ya bayyana cewa a halin yanzu rundunar soji na sa ne da inda Bello Turji yake, inda ya ce ba zai yi ƙarin bayani akai ba.

Daraktan ya ce babu wani sulhu ko tattaunawa tsakanin Bello Turji da jami’an soji, inda ya ce a halin yanzu Turji bashi da wani sukuni kuma ba zai iya tserewa ba saboda tsaro, inda ya ce nan bada jimawa ba rundunar za ta ga bayansa da ayyukansa a yankin Arewa maso yammacin Kasar nan.
