Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa, jam’iyyarsu ta APC ta shirya karɓar wasu jiga-jigan ƴan siyasa daga jam’iyya mai mulkin jihar Kano ta NNPP.

Ganduje ya bayyana hakan ne jiya Lahadi yayin rabon motoci da babura ga shugabannin jam’iyyar APC na ƙananan hukumomi da mazaɓu a jihar Kano, wanda mataimakin shugaban majalisar dattawa kuma sanatan Kano ta Arewa Barau I. Jibrin ya ɗauki nauyi.

Ganduje ya ƙara da cewa rabon kayan ba wai ina na ƴan jam’iyyar APC ba ne, har da dukkan sauran al’ummar jihar, saboda zai bunƙasa rayuwar al’ummar da samar da damarmakin ayyukan yi a tsakankaninsu.

Kowanne shugaban jam’iyya a ƙaramar hukuma ya rabauta da samun mota, yayin da shugabannin jam’iyya a mazaɓu 484 na jihar su ka samu kyautar babura, inda a take a wajen taron kowa ya karɓi takardu da kuma ɗaukar kasonsa.

Yayin da ya ke jawabi a wajen taron Ganduje ya bayyana cewa, dubunnan ƴan jam’iyyar NNPP ne su ke daf da shigowa jam’iyyar ta su ta APC nan ba da daɗewa ba, ciki kuma har da manya-manya ma su riƙe da muƙamai, inda ya bayyana jam’iyyar ta NNPP a matsayin matacciya marar rai.

A nasa jawabin Sanata Barau I. Jibrin ya bayyana cewa, shirin somin taɓi ne kawai na babban rabon kayayyakin da za su yi da aka fara da shugabannin jam’iyya, wanda zai taimakawa al’umma daga rukunai daba-daban.

Leave a Reply

%d bloggers like this: