Mai magana da yawun Shugaba Tinubu kan yada labarai Bayo Onanuga ya bayyana cewa akwai kura-kurai a cikin kalaman da tsohon mataimakin shugaban Kasa Yemi Osinbajo yayi, a gurin kaddamar da littafin tarihin rayuwar tsohon shugaban Najeriya Ibrahim Badamasi Babangida a Abuja.

A yayin kaddamar da Littafin Yemi Osinbajo a cikin wasa ya bayyana cewa shugaba Tinubu ya zo taya masu azabtar da shi murna.
Onanuga ya bayyana hakan ne a yau Talata ta cikin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels.
Onaguna ya ce Babangida ba shi ne mutumin da ya bai’wa shugaba Tinubu kwarin gwiwar shiga harkar siyasa, inda ya ce hakan ba daidai ba ne Osinbajo ya kira Janar Ibrahim Badamasi Babangida a matsayin wanda ya azabtar da shugaba Tinubu a baya.

Acewar Bayo Shugaba Tinubu ba tun yanzu ba yake fadin cewa tsohon shugaban na Najeriya a mulkin soji Janar Ibrahim Babangida ya karfafa masa gwiwar shiga siyasa.

Onanuga ya kara da cewa matsin lamba da Tinubu ya fuskanta ya fara ne a zamanin mulkin Janar Sani Abacha, inda ya ce a wannan lokacin ne shugaba Tinubu da wasu ‘yan siyasa suka yi koƙarin sake kafa majalisar dattawa a Jihar Legas.
Acewar Bayo bayan hawan Janar Babangida mulki ya bijiro da tsarin ‘yan siyasa sababbin jini, wanda hakan ya sanya shugaba Tinubu da wasu mutane da dama, waɗanda tun farko suka kasance a matsayin kwararru da masu zaman kansu a harkokin kasuwanci, suka fito don shiga siyasa.
Wanda hakan ya sanya shugaba Tinubu ya shiga siyasa, hakan ya sanya ya halarci taron kaddamar da litattafin domin girmamawa ga Babangida.