Gwamnatin jihar Kano ta buƙaci shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta fitar da sarki Aminu Ado Bayero daga cikin gidan sarki na Nassarawa.

Mataimakin gwamnan jihar Kwamared Aminu Abdussalam ne ya bayyana haka a gidan gwamnatin jiya yayin da ake bikin raba tallafi da dan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Tarauni Kabiru Dahiru Sule ya bayar.
A cewar mataimakin gwamnan, zaman sarki Aminu Ado Bayero cikin gidan sarki na Nassarawa barazana ce ga Kano.

Ya ce mutanen jihar Kano sun gaji da zaman sarkin a ciki.

Mataimakin gwamnan ya yi zargin jami’an tsaro da harba hayaki mai sa hawaye da amfani da harsashi mai rai wajen tarwatsa wasu masu zanga-zanga.
A cewarsa gwamnan jihar Kano ne kaɗai ke da ikon nada sarki a jihar.
A don haka ya kamata a abar demokaradiyya ta yi aikinta.