Gwamnatin Jihar Yobe ta raba babura 200 ga Ma’aikatan Ma’aikatar aikin gona domin ci gaba da kara bunkasa harkokin noma a Jihar.

Kwamishinan ma’aikatar gona da albarkatun kasa Ali Mustapha Goniri ne ya tabbatar da hakan, a yayin da yake mika baburan ga wadnda suka samu tallafin.

Kwamishina ya bayyana cewa gwamnatin Jihar ta rabawa manoman baburan ne domin
an yi rabon baburan ne domin bunkasa ayyukan ma’aikatan, tare da inganta noman zamani ta hanyar samar da sabbin kayan aiki a Jihar.

Kazalika Kwamishinan ya ce Ma’aikatarsa za ta sanya idanu akan yadda Ma’aikatan za su gudanar da ayyukan bunkasa harkokin noman don tabbatar da ganin cewa manoman da ke dukkan lungu da sako na jihar na gudanar da noman da iri masu inganci.

Bugu da kari ya ce an bai’wa ma’aikatan horo, ta yadda za su kara kaimi wajen kara kulla alaka tsakanin masu bincike da manoma, domin habaka kara samar da kayayyaki, da kuma tabbatar da samar da wadataccen abinci, da kuma inganta rayuwar manoma.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: