Hukumar karbar korafe korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano ta kama shugaban Karamar hukumar Kiru Abdullahi Muhammad bisa zarginsa da sayar da wani fili da aka samar domin gudanar wasa na Kafin Maiyaki Mini Stadium.

A wani bincike da hukumar ta gudanar ta gano cewa wani Kamfani mai suna Mahasum ne ya sayi filin akan kudi sama da naira Miliyan 100, inda kuma Kamfanin ya tura kudaden kai tsaye cikin asusun shugaban Karamar hukumar.
Mai magana da yawun hukumar Kabir Abba Kabir ya ce an tabbatar da cewa daga ranar 1 ga watan Nuwamban 2024 zuwa ranar 27 ga wata Fabrairun 2025, an zuba akalla Naira Miliyan 240 a cikin Asusun shugaban Karamar hukumar ta Kiru.

Kakakin ya ce hakan ne ya sanya hukumar ta dauki matakin gaggawa na gudanar da bincike akan zargin.
Acewarsa bayan binciken hukumar ta kwato dukkan kudaden da aka biya, don ganin an mayar da kudaden inda suka da ce.

Wasu rahotannin sun bayyana cewa a halin yanzu shugaban Karamar hukumar ta Kiru na ci gaba da bai’wa jami’an hukumar hadin kai wajen gudanar da bincike akan batu, tare da gano dukkan masu hannu a ciki.