Rundunar ‘yan sandan Jihar Lages ta tabbatar da kama wasu mutane 35 da ake zargi da aikata fashi a titi a yankunan Ajah da Elemoro a Jihar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Benjamin Hundeyin ne ya tabbatar da kamen ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar.
Benjamin ya ce jami’ansu da ke gudanar da sintiri a yankunan Ajah da Elemoro ne suka kama mutanen, a lokacin da suka kai wani sumame.

Kakakin ya ce akwai wasu tawagar sintiri a sassan jihar da ke gudanar da irin aikin na yaki da aikata miyagun laifuffuka a fadin Jihar.

Mutanen da jami’an suka kama a ranar 24 ga watan Fabrairun da ya gabata, sun hada da Alao Oluwafemi, Adeshina Akinrinde, Udoh John, Afolabi Kola, Daniel Augustine, da kuma Olalekan Qudus.
Sauran su ne Bashir Umar, Nasiru Muhammed, Ashiru Sanni, John James, Adebayo Oyebode, Aminu Abubakar, Abdullahi Ibrahim da Jamilu Usman, inda jami’an suka kama su a lokacin da suke gudanar da sinitiri.
Kakakin ya ce an kama mutanen ne a cikin mako guda, inda kuma aka gurfanar da su a gaban kotu domin girbar abinda suka shuka.
