Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa NLC ta umarcin dukkan ƴaƴanta da su zama cikin shiri don gudanar da zanga-zanga a faɗin Najeriya, idan har gwamnatin tarayya ta aiwatar da ƙarin kuɗin kira da na Data a kamfanonin sadarwa, saɓanin sharuɗan da su ka amince da su a yarjejeniyarsu.

Tare da gargaɗin cewa duk wani yunƙuri na karkasa masu amfani da wutar lantarki daga hukumar kula da wutar lantarkin, shi ma ba za a lamunta ba.

Kamfanonin sadarwa dai na wayoyin hannu sun bayyana cewa su basu san da wata yarjejeniya da aka cimma ba tsakanin ƙungiyar ƙwadago da kuma gwamnatin tarayya, ta wajen rage ƙarin daga kashi 50 cikin 100 zuwa kashi 35 cikin 100.

Wannan matakin na ƙungiyar ƙwadagon na zuwa ne dai biyo bayan taron majalisar zartarwarta a birnin Yolan jihar Adamawa, inda su ka tattauna akan matsin tattalin arziƙin da ya ke addabar ma’aikata a faɗin ƙasar.

Cikin jawabin dai da aka sanar a jiya Lahadi, ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa, duk wani ƙarin kuɗi da aka sake aka yi a ɓangaren wutar lantarki, zai janyo babbar turjiya daga gare su.

Ta kuma yi kira ga dukkan sauran ƙungiyoyi na kamfanoni da na ci gaban al’umma, da su zama cikin shirin yin gagarumar zanga-zanga don yaƙar tsarin da zai cutar da al’umma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: