Gwamnan jihar Ribas Siminilaye Fubara ya umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta a jihar da ta shirya zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin jihar.

Gwamnan ya ce ya bi umarnin kotun koli duk da cewar bai gamsu da hukuncin da ta yanke ba.

Fubara a wani bayani da gwamnan ya yi wa al’ummar jihar, ya ce bai gamsu da hukuncin kotun kolin ba.

Amma su na dakon sahihin hukuncin kotun da za su samu zuwa ranar Juma’a 7 ga watan Maris ɗin da mu ke ciki.

Sannan ya ce za su yi biyayya ga hukuncin duk da ba su gamsu da shi ba.

Gwamnan ya umarci shugabannin kanana hukumomi masu barin gado da su mika ragamar mulki a yau Litinin.

Sannan ya bayar da sabon umarni don ganin an sake shirya zaɓen ƙananan hukumomi 23 da ke jihar.

Kotun koli ta tushe zaben da aka yi a jihar biyo bayan gaza cika sharudan da ya kamata a samu a cikinsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: