Majalisar dokokin jihar Legas ta sake zaɓen Mudashiru Obasa a matsayin kakakinta, kusan watanni biyu kenan bayan tsige shi a watan Janairu.

An sanar da Sake zaɓen nasa ne dai a majalisar yau Litinin, bayan kakakin majalisar Moji Meranda ta yi murabus daga kan kujerarta, sakamakon shafe makonni ana taƙaddama a majalisar kan shugabancin.
Obasa ya bayyana tsigeshin da aka yi a matsayin wani wasan kwaikwayo, sakamakon aiwatar da hakan bisa rashin ƙa’ida.

Sai dai kuma ya tabbatar da cewa ba zai hukunta kusan ƴan majalisu 30 da su ka goyi da bayan tsigeshin ba, tare da cewa dukkansu ƴan uwansa ne.

Mojisola Meranda ta yi murabus daga kan kujerar ne a yau Litinin, bisa abinda da aka bayyana a matsayin umarni daga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Ta kuma saukan ne don samar da haɗin kai a zauren majalisar, da kuma babbar jam’iyya mai mulki ta APC.
An ruwaito cewa tun biyo bayan tabbatar da ita a matsayin kakakin majalisar, ba a barta ta shiga gidan da aka ware a hukumance gare ta ba da ke Ikejan jihar Legas, sakamakon tsohon kakakin majalisar ya ƙi fita daga gidan.