Wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da wani jami’in dan sanda mai suna Modestus Ojiebe akan babban titin Abuja zuwa Kaduna a birnin tarayya Abuja.

Jami’in na aiki ne da rundunar ‘yan nsandan Jihar Kwara, ‘yan bindigan sun yi garkuwa da shi ne a Kusa da Unguwar Dei-Dei da ke kusa da barikin ‘yan sanda da ke Abuja.

Mai sharhi kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi Zagazola Makama ya bayyana cewa maharan sun sace jami’in ne a lokacin da ya tsaya domin duba motarsa da ta samu matsala.

Ya ce Maharan sun zo ne a cikin mota, inda suka kwace masa wayarsa da ta matarsa da na’urar cirar kudi ta ATM, yayin da daga bisa bayan sun lura cewa jami’in tsaro ne suka tafi dashi suka bar matarsa.

Sai dai bayan yin garkuwa da shi tuni aka aike da jam’an tsaro domin kubtar da jami’an daga hannun maharan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: