Hadakar jami’an tsaro a Jihar Kebbi sun samu nasarar hallaka shugaban kungiyar ‘yan Lakurawa wadda ake kira da Maigemu a Jihar.

Mai sharhi kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi Zagazola Makama ne ya tabbatar da hallaka Maigemu a wata wallafa da ya fitar a yau Juma’a.

Makama ya ce jami’an sun samu nasarar hallaka shine a jiya Alhamis, a yankin Kuncin Baba da ke Karamar hukumar Arewa a Jihar bayan yin musayar wuta.

Zagazola ya kara da cewa Nasarar na samu ne mako guda kenan bayan wata Ziyara da gwamnan Jihar Nasir Idris ya ziyarci yankunan Bagiza da Rausa Kade da ke cikin karamar hukumar.

Gwamna Nasir ya ziyarci yankunan ne domin jajantawa al’umomin yankin sakamakon hallaka mutane shida mayakan na Lakurawa suka yi a yankunan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: