Jam’iyyar PDP ta Kasa ta yi Allah-Wadai da dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da Majalisar Dattawa ta yi daga cikin na tsawon watanni shida, bayan ta zargi shugaban Majalisar Sanata Godswill Akpabio da yunkurin cin zarafinta.

 

A cikin wata sanarwa a Jam’iyyar ta fitar a yau Juma’a, ta nuna rashin jindadinta bisa matakin dakatarwar da Majalisar ta yiwa Natasha.

Acewar Jam’iyyar dakatar da Natasha ba tare da gudanar da bincike ba, hakan na nuni da cewa Majalisar na kokarin boye zargin da ta ke yiwa Akpabio ne.

Sanarwar wadda mai magana da yawun jam’iyyar na Kasa Debo Ologunagba ya fitar, ya kara da cewa Dakatarwar hakan zai tauye hakkin al’ummar da ta ke Wakilta.

 

Ologunagba ya bayyana cewa kamata ya yi Akpabio ya fito ya kare kansu akan zarge-zargen da Natasha ta yi masa , tare da sauka daga jagorantar tattaunawa akan batun.

Sanarwar ta ce hakan babbban abin kunya ne da takaici a samu shugaba Majalisar ta Dattawa da yunkurin cin zarafi, wanda hakan kuma ka iya bata sunan Majalisar.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: