Kungiyar kiristoci ta Kasa CAN ya bukaci da a zauna Lafiya tsakanin addinai a Najeriya.

Shugaban Kungiyar na Kasa Daniel Okoh ne ya bayyana hakan a Abuja a gurin liyafar buda baki da ya halarta a jiya Alhamis wanda Masallacin Alhabiyya ya shirya.

Masallacin na Al-Habibiyya ya shirya liyafar buda bakin ne tare da ciyar da mabuta 2,300 abincin buda baki.

Acewar Okoh Musulmi da Kirista abu guda ne, inda ya bukaci ga ‘yan Najeriya da su kara fahimtar juna don kara tabbatar da zaman lafiya da martaba juna.

Shugaban na CAN ya kuma yabawa Masallacin bisa shirin ciyar da masu Azumi da suka samar, inda ya bayyana cewa hakan na kara samar da zaman Lafiya a tsakanin al’umma da kuma manyan addinai biyu da ake da su a Kasar nan.

Shugaban kungiyar ya ce shirin ciyarwar ya na da kyau, kuma hakan na kara karfafa alaka tsakanin addinai, inda ya bukaci ‘yan Najeriya da su fahimci addinan junansu, wanda hakan zai samar da hadin kai.

Babban Limamin Masallacin Sheikh Fuad Adeyemi, ya bayyana cewa shirin ciyarwar na taimakawa mabukata ba tare da yin duba da addininsu ba.

A yayin buda bakin kungiyoyin addinai da manyan mutane da dama ne suka halarci taron buda bakin, da nufin kara inganta alaka da fahimtar juna don kara tabbatar da zaman lafiya a fadin Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: