Wasu da ake zargi masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da wasu mutane Bakwai ciki harda mata da kananan yara a Kauyen Anchuna da ke Masarautar Ikulu a karamar hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Larabar da ta gabata, inda sukai ta harbe-harbe, bayan mamaye Kauyen da suka yi, wanda hakan ya ba su damar tafiya da mutanen.

Wani mazaunin yankin mai suna Samuel Kukah ɗa ga Bishop Hassan Kuka ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce daga cikin wadanda ‘yan bindigan suka sace harda dan uwansa mai suna Ishaya Kukah.

Samuel ya bayyana cewa dan uwannasa shi kadai ne Namiji a cikin wadanda ‘yan bindigan suka yi garkuwa da su, inda ya bayyana cewa sauran mutanen mata ne da kananan yara.

Acewarsa maharan sun sace su ne da misalin karfe 11 na dare, inda ya ce har kawo yanzu maharan su tuntube su ba domin neman kudin fansa kafin sakin su ba.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: