Ministar Harkokin Mata Imaan Suleiman Ibrahim ta bayyana aniyarta na sulhunta shugaban Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan bisa rikicin da ke faruwa a tsakaninsu.

Ministar ta bayyana hakan ne ga manema labarai bayan taron bikin Ranar Mata ta Duniya.
Imaam ta nuna damuwarta bisa dakatarwar da Majalisar ta yiwa Sanata Natasha, inda ta ce ko kadan hakan bai haka mai dace ya faru ba.
Ministar ta bayyana cewa a Majalisar baya da ana da sanatoci mata Tara, inda kuma a yanzu hudu ne kadai su kai saura a Majalisar.

Acewarta ko kadan ba sa son rasa kowacce Mace a cikin Majalisar, sai dai bukatar kara neman dadi.

Ministar ta kara da cewa a halin yanzu ana ci gaba da kokarin ganin an daidaita lamarin, don tabbatar da zaman lafiya ta hanyar tattaunawa da duk masu ruwa da tsaki, tare da kuma da tabbatar da cewa an yiwa kowa adalci.
Kazalika ta ce za su tabbatar da ganin sun shiga tsakani bangarorin biyu don samar da hadin kai tsakanin maza da mata a shugabnci.