Gwamnatin Jihar Kebbi ta dauki Malamai sabbin malaman Makaranta 2,000 a kokarin da ta ke yi na inganta fannin Ilmi a Jihar.

Kwamishinar ilmi ta Jihar Dr Halima Muhamma Bande ce ta tabbatar da hakan ga manema labarai.

Kwamishinar ta ce an dauki malaman ne bisa kokari da jajircewar gwamnan Jihar Nasir Idris ya ke yi na inganta bangren ilmin Jihar.

Dr Halima ta kara da cewa daga cikin malaman da za a dauka 391 ne aka zaba a matakin farko, inda ta ce wadannan aka dauka din sun mallaki shaidar digiri, da HND tare da takardar kammala karatun digiri na biyu inda za a tura su makarantu daban-daban a fadin jihar.

Kwamishinar ta kuma ce za a sake fitar da jerin sunayen wasu malamai da aka dauka, wadanda suka mallaki takardar NCE.

Kazalika ta ce kwamitin da ke aikin daukar malamai ya karbi takardun neman aiki na mutane 18,000, inda ta ce takardu 4,000 kadai suka samu shiga matakin tantancewa, inda ta ce za a ci gaba da daukar karin malamai domin cike gurbin da ake da shi a makarantu.

Bande ta yi kira ga sababbin malaman da su mayar da hankali wajen koyar da daliban domin ci gaban ilimi a jihar Kebbi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: