Jam’an sojin Najeriya na rundunar Operation Fasan Yanma sun dakile wani yunkurin wasu ‘yan bindiga na kokarin sace mutane da suka yi a ƙaramar hukumar Kankia ta jihar Katsina.

Mai sharhi kan sha’anin tsaro a yankin Tafkin Chadi Zagazola Makama ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata wallafa da ya fita a yau Asabar.
Makama ya ce jami’an sun kuma samu nasarar ceto wani mutum daya da maharan suka yi yunkurin sacewa, inda kuma suke kokarin kubtar da wasu mutane biyu da maharan suka sace.

Wasu Majiyoyi sun shaidawa Makama cewa lamarin ya faru ne a jiya Juma’a, bayan maharan sun shiga Kauyen Mashayay da ke Jihar, inda suka harbi wani mutum mai suna Lado Mekaji a duka Kafarsa, tare kuma da kwace wayoyi da kudade mazauna garin.

Daga bisani kuma Maharan suka nufi Kauyen Kolawa, suka yi garkuwa da wata mata mai suna Aisha da kuma wani mai suna Bello.
Makama ya kara da cewa bayan samu rahoton faruwar lamarin jami’an sojin na Oparetion Farsar Yanma, hadi da na sa-kai suka gaggauta zuwa yankin domin kubtar da wadana maharan suka yi garkuwa da su.
Bayan bin sahun maharan jam’an sun kubtar da Lado Mekaji, inda aka mikashi ga Asibiti domin kula da lafiyarsa, inda jami’an ke kokarin kubtar da Aisha da Bello daga hannun maharan.