Majaliar Dattawa ta bayyana cewa ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan daga Majalisar ne ba don zargin cin zarafin da ta yiwa Shugaban Majalisar Sanata Godswill Akpabio ba , sai don sabawa dokokin majalisar da aka same da yi.

Shugaban Masu rinjaye na Majalisar Sanata Bamidele Opeyemi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar.

Opeyemi ya bayyana cewa Majalisar ta dauki matakin dakatar da Sanata Natasha ne bisa sabawa ka’idoji da dokokin Majalisar da ta yi.

Sanarwar ta kara da cewa wadannan dalilai ne kadai suka sanya aka dakatar da ita ba don wani abun ba.

Kazailaka Opeyemi ya ce da ba a samu Sanata Natasha da rashin da’a da kuma karya dokokin Majalisar ba, Majalisar za ta yi duba akan korafin da ta gabatar mata kamar yadda doka ta bada dama.

Ya ce rashin bin ka’ida da Sanatar ta yi ne, ya sanya Majalisar ta dauki matakin dakatar da ita, bayan shawarar kwamitin da’a ya yanke shawawar dakatar da ita.

Acewarsa Kwamitin ya same da laifin sabawa sashi na 6.1 da kuma sashi na 6.2 na dokokin majalisar, wanda hakan ya sa aka dakatar da ita.

Opeyemi ya ce an kuma samu Sanatar aikata Laifuka Biyar, ciki harda kin zama akan kujerar da aka canza mata a yayin zaman Majalisar na Ranar 25 ga watan Fabrairu, tare da yin magana ba tare da yarjewar shugaban Majalisar ba.

Sannan ya ce an same da yin kalaman da ba su kama ba ga shugaban Majalisar, inda ya ce wadanda su ne ginshikan da suka sanya aka dakatar da ita.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: