Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Legas da kuma ta Yola da ke Jihar Adamawa, sun yanke wa wasu dillalan miyagun kwayoyi huɗu da aka kama da safarar ƙwayoyi daurin shekaru 95 a gidan ajiya da gyaran hali bayan jami’an NDLEA sun gurfanar da su.

Kwayoyin da aka kama a hannuj mutanen darajarsu ta kai ta Naira biliyan 4.6.
Jami’an hukumar ta NDLEA sun kama Guda daga cikin wadanda aka yankewa hukuncin mai suna Ogbuji Christian Ifeanyi a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Jihar Legas a shekarar da ta gabata.

Jami’an sun kamashi e a lokacin da yake koƙarin shigowa da hodar iblis dauri 817 mai nauyin akalla kilogram 20 da kudinta ya kai naira biliyan 46.

Hukumar ta ce ba wannan ne karo na farko ba da ta taba kama Ogunji ba, inda watanni 16 ma da suka gabata sai da aka kamashi da zargin safarar kwayoyi.
Sauran mutanen sun haɗa da Iloduba Augustine Chinonye, Shuaibu Nuhu Is, da kuma Zidon Zurga.
Baya daurin shekaru 95 da aka yanke musu, an kuma ci tarar su Naira miliyan 25, inda kotu ta umarci da a ƙwace motocin da aka yi amfani da su wajen safarar ƙwayoyin.
A wata sanarwa da kakakin hukumar Femi Babafemi ya fitar a jiya Juma’a ya bayyana cewa shugaban hukumar Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya) ya yaba da hukuncin kotu da kuma ƙoƙarin jami’an NDLEA wajen kama masu safarar miyagun ƙwayoyi a Najeriya.