Hukumar kula da hakar mai a Najeriya NMDPRA ta bayar da lasisin bude sabbin matatun man fetur guda uku a Kasar nan.

Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta Fitar a yau Asabar.
Shugaban Hukumar Farouk Ahmad ya bayyana cewa hukumar ta bayar da lasisin gina sabbin matatun ne a Jihohin Abia, Delta da KUMA kuma Edo.

Sanarwar ta bayyana cewa za a bude Matatar Eghudu da za ta iya tace ganga 100,000 a kowacce rana a Jihar Edo, inda kuma za a bude Matatar MB da za ta dunga tace ganga 30,000 a kowacce rana a Jihar Delta.

Sannan Matatar HIS kuma za ta dunga tace ganga 10,000 a kowacce rana a Jihar Abia.
Hukumar ta bayyana cewa da zarar an kammala sabbin matatun ukun za su iya tace ganga 140,000 na man fetur kowacce rana.