Shugaban Kasa Bola Tinubu ya nada Tsohon shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa INEC, Farfesa Attahiru Jega a matsayin mai bashi shawara da kuma Kula da Shirin Gyaran Noma da Kiwo na Shugaban Ƙasa.

Mai magana da yawun shugaban Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da yafitar a jiya Juma’a.
Sanarwar ta bayyana cewa shugaba Tinubu na fatan naɗi zai kawo ci gaba a harkar noma da kiwo, tare da ƙarfafa yunƙurin raya ƙasa.

Farfesa Jega dai ya kasance mataimakin shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan gyaran Noma da Kiwo tare da Shugaba Tinubu, inda Kwamitin ya gabatar da shawarwari kan yadda za a inganta harkar noma da kiwo, ciki har da kirkirar Ma’aikatar Kiwo, wacce a halin yanzu ke da minista.

Onanuga ya ce nadin Jega a matsayin mashawarci na musamman zai taimaka wajen ci gaba da aiwatar da shirin gyaran noma da kiwo da kuma tabbatar da nasarorin da aka riga aka samu.