Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya tabbatar da kudurin na cewa zai tabbatar da ganin ya Jiharsa ta samu ingantaccen yanayi kafin barinsa mulkin Jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kaddamar da ginawa da kuma fadada titunan garin Zari’a a Jihar.
Uba Sani ya ce zai yi kokarin wajen ganin Jihar Kaduna ta gyara fiye da yadda ya same ta a lokacin da ya karfi mulki.

Acewarsa a halin gwamnatinsa ta mayar da hankali akan shirin farfado da yankuna Karkara, inda ya ce gwamnatin ta kaddamar da ayyukan gina tituna sama da 78 a fadin jihar tun bayan karbar ragamar Jihar.

Bugu da kari gwamnan ya ce ayyukansa na tafiya yadda ya kamata, bisa an samar da wadattun kudade ga ‘yan kwangila domin kammala su akan lokacin da aka tsara.
Ya ce samar da titunan hakan zai kara inganta harkokin kasuwanci, tare kuma da kara tabbatar a tsaro afadin Jihar.
