Jam’iyyar APC a Jihar Kaduna ta bayyana cewa ko kadan ba ta da wata damuwa bisa sauya shekar da tsohon gwamnan Jihar Malam Nasir El’rufa’i zuwa jam’iyyar SDP ba.

Sakataren Jam’iyyar na Jihar Alhaji Yahya Baba-Pate ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa a yau Litiinin.
Jam’iyyar ta ce a halin yanzu ta mayar da hankali ne akan nasarar shugaban Kasa Bola Tinubu da gwamna Uba Sani a zaben shekaarar 2027 da ke tafe.

Baba-Pate ya kuma nuna gamsuwarsa da yadda jam’iyyar ke kara ƙarfi a jihar, yana mai cewa gogaggun ‘yan siyasa na ci gaba da shigowa cikin jam’iyyar ta APC a ko da yaushe.
