Dan takarar shugaban Kasa a jam’iyyar SDP a zaben 2023 da ya gabata Adewole Adebayo ya taya tsohon gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El’rufa’i murnar shigowa jam’iyyarsu ta SDP.

Adebayo ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin.

Adeboya ya ce jam’iyyar ta SDP, tare da mambibinta na maraba da shigar El’rufa’i cikinta, wanda hakan babbar nasara ce.

Dan takarar shugaban Kasar ya bayyana cewa shigwar El’rufa’i jam’iyyar hakan zai ba su damar hada kai dashi wajen kawo karshen Matsalar tsaro da kuma yaki da Talauci a Najeriya.

Tsohon gwamnan na Kaduna ya koma jam’iyyar ta SDP daga jam’iyyarsa ta APC a yau Litinin, ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: