Gwamnan jihar Rivers Siminilaye Fubara ya sake aikewa da wasika ga majalisar dokokin jihar don sake zuwa gabatar da kasafin kudin shekarar da mu ke ciki.

Gwamnan ya ayyana Laraba 19 ga watan Maris da mu ke ciki don zuwa majalisar.

A wata wasiƙa da gwamnanya aikewa da kakakin majalisar, gwamnan ya yi bayanin zuwansa majalisar a ranar 12 ga watan Maris wanda aka hanashi shiga majalisar
Gwamnan ya ce ƙoƙarin da ya yi na zuwa biyayya ce ga hukuncin kotun ƙoli ta ƙasar da ta umarceshi ya sake bayyana don gabatar da kasafin.

Gwamnan ya buƙaci dukkan mahukunta a gwamnati da su yi aiki bisa doka da kuma bin kundin tsarin mulki domin al’ummar jihar.

Idan za a iya tunawa gwamna Fubara ya bayyana a gaban majalisar ranar Laraba da ta gabata don gabatar da kasafin kudin jihar sai dai aka hanashi shiga.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: