Gwamnatin Jihar Kano ta ce Kotun Daukaka Ƙara da ke Abuja ba ta soke sake nadin Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano ba.

Kwamishinan shari’a na Jihar Haruna Isa Dederi ne ya bayyana hakan ga manema labarai, yana mai cewa kotun ta dakatar da hukuncin da ta yanke ne na ranar 10 ga watan Janairu ne kadai ba soke nadin Muhammad Sanusi ba, har zuwa lokacin da Kotun Koli za ta yanke hukuncin karshe akan rikicin.

Dederi ya kara da cewa Kotun Koli ce kadai ke da ikon canja hukuncin komawar Sanusi ll Masarautar Kano.

Kwamishinan ya ce kotun ta tabbatar da cewa gwamnatin jihar Kano na da hurumin mayar da Sanusi kan karagar Masarautar Jihar, inda ya ce har yanzu Muhammad Sanusi na nan a Matsayin sarkin Kano har zuwa lokacin da kotun Koli za ta yanke hukunci.

Wannan dai na zuwa ne bayan da a jiya Juma’a kotun daukaka kara ta dakatar da hukunci da Kotun tarayya ta yanke a ranar 10 ga watan Janairu 2025, inda ta ce Kotun ba ta da hurumin yanke hukunci kan rikicin.

Sannan Kotun ta kuma bayar da umarni kowa ya ci gaba da zama akan matsayinsa har sai kotun kolin ta yanke hukuncin..

Leave a Reply

%d bloggers like this: