Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta musanta zargin da tsohon gwamnan Jihar Malam Nasir Elrufa’i ya yi na cewa Jami’an tsaro sun sace Tsohon Kwamishinasa Malam Jafaru Sani.

A wata wallafa da Elrufa’i ya fitar, ya bayyana cewa Jami’an tsaron sun dauke Kwamishinan ne sakamakon sauya shekar da ya yi daga Jam’iyyar APC zuwa SDP.

El-Rufai wanda ya yi gwamna a Kaduna daga shekarar 2015 zuwa 2023, ya bayyana cewa Kungiyar masu garkuwa da mutane da ke da bayyana kansu a matsayin ‘yan sanda, kuma masu alaka da gwamna mai ci Uba Sani ne suka dauke tsohon Kwamishinan.

Acewarsa Kotun majirtire ta tsare shi a gidan gyaran hali, ba tare da bayyana rahoton binciken farko daga Jami’an ‘yan sanda ba ko kuma zarge-zarge daga Ma’aikatar Shari’a ta Jihar ba.

Sai dai a wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Mansur Hassan ya fitar a jiya Juma’a, ya musanta zargin na Elrufa’i, ya ce babu wata Kungiyar masu garkuwa da mutane a rundunar ’yan Sanda ta Najeriya.

Mansur Hassan ya ce rundunar ‘yan sanda, hukuma ce da ke Karkashin kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, da ke tabbatar da bin doka da oda, inda ya ce dukkan wani wanda ake zargi da aikata laifi jamian ‘yan sanda na da ikon kama shi tare da yin bincike da gurfanar da shi a gaban kotu.

Kakakin ya bukaci ‘yan siyasa da su kaucewa yin irin wadannan kalaman marasa tushe, wanda ka iya haifar da rudani ga sha’anin tsaro.

Ya ce dukkan wani mai korafi ya bi hanyar shari’a maimakon yin irin wadannan kalaman da ka iya tayar da tashin hankali.

Leave a Reply

%d bloggers like this: