Kimanin mutane Falasɗinwa 326 ne su ka rasa rayukansu, biyo bayan wani sabon hari da ƙasar Isra’ila ta kai duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsawon watanni biyu.

Harin da aka kai a yau Talata ya auku ne a Gaza, ciki har da yankunan Khan Younis da Rafah da ke kudanci da Arewacin na birnin Gaza, da kuma yankin Deir El-Balah da ke tsakiyar birnin.
Da yawa daga cikin waɗanda aka kashe a harin, sun kasance ƙananan yara ne.

Ministan lafiya na Falasɗin ya shaida cewa, an isa da gawarwakin kimanin mutane 326 zuwa asibitoci a zirin Gaza, tare da kuma ci gaba da kawo waɗanda harin ya rutsa da su.

A ɓangarenta ƙungiyar mayaƙan Hamas ta ƙasar Falasɗinun, ta ce harin na Isra’ila ya zamto tamkar soke yarjejeniyar tsagaita wuta ne da aka fara tun 19 ga watan Janairu.
Hamas ta kuma yi kira ga ƙasashen Larabawa, Musulmai da sauran al’ummar duniya, da su fito su nuna rashin goyon bayansu ga wannan zaluncin.
Ƙungiyar Jihar ta IPU da ke Falasɗin, ta yi zargin cewa ƙasar ta Isra’ila ce ke yin dukkan wani yunƙuri na lalata yunƙurin cimma tsagaita wuta.
A gefe guda firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce shi ne ya bai’wa sojoji umarnin kai harin, sakamakon ƙin sakin wasu ƴan ƙasar Isra’ila da su ke hannun mayaƙan Hamas.
