Majalisar koli ta harkokin addinin Muslunci a Najeriya, karkashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na lll ta musanta rade-raden da ke yawo cewa ta na shirin musluntar da Najeriya.

Mataimakin mai bai’wa Majalisar ta harkokin addinin muslunci shawara kan harkokin shari’a Imam Haroun Muhammad Eze ne ya musanta batun ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.
Sanarwar ta bayyana cewa rade-raden da ake yadawa a shafukan sada zumunta na nuni da cewa Sarki Musulmin Alhaji Sa’ad na shirye-shiryen musluntar da Najeriya, inda ya ce ko kadab babu gaskiya a cikin rahotannin.

Sanarwar ta bayyana cewa a halin yanzu Alhaji Sa’ad ba ya gida Najeriya ya tafi zuwa kasashen waje sama da makwanni biyu da suka wuce.

Eze ya ce kafatanin rahotan babu gaskiya a cikinsa, yana mai cewa Sarkin Musulmin ya kasance ba iya musulmi kadai ya ke jagoranta ba harda sauran Kabilun Najeriya daban-daban.
Har ila yau ya ce masu yada irin wannan jita-jitar su na yi ne domin raba kan al’umma, inda ya ce hakan ne ya sanya Majalisar kolin ta dauki matakin musanta batun, don kada wasu su dauki batun a matsayin gaskiya.