Gwamnan Jihar Ebonyi Francis Nwifuru ya dakatar da wasu masu taimaka masa mutum biyu daga bakin aiki, bisa zarginsu rashin da’a da kuma aikata cin amanar aiki.

Sakatariyar gwamnatin Jihar Farfesa Grace Umezurike ce ta tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ta fitar yau Talata.
Sakatariyar ta bayyana cewa gwamnan ya dakatar da hadiman na shi ne bayan tabbatar da sun aikata laifin da ya sabawa ka’idar aikin gwamnatin Jihar.

Kazalika sanarwar ta bayyana cewa an kuma umarci hadiman gwamnan da aka sallama da su mika dukkan wani kayan gwamnatin Jihar da ke hannunsu ga ofishin sakataren gwamnatin Jihar a yau Talatar.

Ta ce hadiman da gwamnan ya dakatar sun hada da mai bashi shawara na musamman kan tsaron filayen jirgin saman Jihar, da kuma babban mataimakin gwamnan na musamman kan sha’anin tsaro a yankin Ebonyi ta Arewa.
Sakatariyar ta ce gwamnatin ta yi hakan ne domin tabbatar da kawo karshen rashin da’a da wasu ma’aikatan ke yi.
Dakatarwar da gwamnan ya yiwa hadiman na sa na zuwa ne kwana guda bayan da gwamnan ya dakatar da wasu kwamishinoninsa uku, tsawon wata guda bisa rashin halartar taron majalisar zartarwar Jihar da ba su yi ba, ba tare da bayar da wani dalili ba.