Majalisar wakilan Najeriya sun miƙa kyautar kuɗi kimanin Naira miliyan 750 ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a ƙoƙarinsu na ci gaba da nuna goyon bayansu gareshi.

Kakakin majalisar wakilan Tajudden Abbas ne ya miƙa shaidar karɓar kuɗin ga shugaban, a madadin sauran ƴan majalisun.
Lamarin ya auku a jiya Litinin, lokacin da shugaba Tinubu ya shirya taron buɗa bakin azumin Ramadan ga shugabanni da mambobin majalisar a fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja.

Abbas ya bayyana cewa kuɗaɗen kashi 50 ne cikin 100 na albashin ƴan majalisun na tsawon watanni shida da su ka sadaukar, don ƙara ƙaimi ga ayyukan jin ƙai da taimakon marasa galihu da shugaban ya ke yi a faɗin Najeriya.

Tajudden ya kuma godewa shugaban bisa gayyatar su zuwa taron buɗe bakin, tare da cewa a koda yaushe ya na nuna kulawa da girmamawa ga ƴan majalisun.
A ƙarshe ya buƙaci ƴan Najeriya mabiya addinin Musulunci da Kirista, da su yi amfani da wannan lokacin na azumin watan Ramadan wajen yi wa ƙasar nan Addu’o’i.