Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da kudirin dokar haraji da shugaba Bola Tinubu ya gabatar ga Majalisun dokokin Kasar, bayan ya tsallake karatu uku.

Majalisar ta amince da kudurin ne a yau Talata, bayan kammala yin nazari sosai akansa a ranar Alhamis din da ta gabata.


Idan ba a manta ba a watan Oktoban shekarar 2024 da ta gabata ne dai shugaban Kasa Bola Tinubu ya aikewa da Majalisun dokokin Kasar kudirin dokar harajin don amince masa aiwatar da ita.
Kafin amincewa da kudurin sai da Kwamitin kudi na Majalisar ya gudanar da taron jin ra’ayoyin mutane kan lamarin, daga bisani kuma bayan kammala sauraron ra’ayoyin mutanen Kwamitin tattara ra’ayoyin mutane tare da mikawa Majalisar.
Dokar Harajin dai ta kunshi kudurori hudu, da suka hadar da kudurin dokar kafa hukumar tattara haraji mai suna Nigeria Revenue Service, da hukumar hadaka da tattara haraji da ƙudirin haraji na Najeriya da kuma kudirin dokar tafiyar da haraji ta Najeriya.
