Sakataren gwamnatin tarayya George Akume, ya nesanta kansa daga binciken da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta ke yi wa mai taimaka masa na musamman Andrew Uchi.

Rahotanni sun bayyana cewa dai tuni Uchin ya na tsare a hannun hukumar ta EFCC, sakamakon zargin cin hanci da rashawa, da kuma mallakar kuɗaɗen da yawansu ya kai Naira miliyan dubu goma.

Ana kuma dai zargin nasa da mallakar kadarori da kuɗin su ya kai Naira miliyan dubu shida a biranen Abuja, Jos, da kuma ƙananan hukumomin Makurdi, Gboko da Tarka a jihar Binuwai.

Cikin wata sanarwa da aka fitar jiya Litinin ta hannun daraktan yaɗa labarai da hulda da jama’a na ofishin sakataren gwamnatin Segun Imohiosen, ya ce sakataren gwamnatin tarayyar ya tabbatar da ƙudurinsa na wanzar da buɗaɗɗe da kuma nagartaccen shugabanci.

Ya kuma bayyana cewa abu ne mai muhimmanci a sanar da cewa ofishin ba shi da hannu a cikin wannan zargin na rashin ɗa’a, kamar yadda ko yaushe su ke akan gaskiya da nagartar aiki.

Ya buƙaci hukumar ta EFCC da ta tabbatar an hukunta duk wanda aka samu da laifi, tare da buƙatar al’umma kar su yi hanzarin yanke hukunci akan batun duba da har yanzu ana kan yin bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: