Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar Rivers, bayan dakatar da gwamna Siminilaye Fubara da majalisar dokokin jihar.

Shugaban ya bayyana hakan ne a yammacin yau Talata a wani jawabi da ya yi ga ‘yan Kasar, bayan wata ganawa da shugabannin hukumomin tsaron Kasar kan wani hari da aka kai kan bututun man fetur a Jihar ta Rivers.

Shugaban ya kuma bayyana Navy Vice Marshal Ibok-Ete Ekwe Iba a matsayin gwamnan riko na Jihar.

A jawabin na Tinubu ya bayyana yadda aka rushe ginin majalisar dokokin Jihar watanni 18 da suka gabata, wadda aka kasa gaza sake gina ta har zuwa yanzu.

Shugaban ya kara da cewa tun bayan rikice-rikicen da ke faruwa a Jihar ta Rivers Jihar ta tsaya cak, kuma hakan ya nuna cewa an tauyewa mutanen Jihar hakkinsu na dimkradiyya.

Shugaban ya ce kafin daukar wannan mataki yayi iya bakin kokarina wajen ganin an samu tabbataccen zaman lafiya da magance matsalar amma hakan ya ci tura ga dukkan ɓangarorin da ake rikicin inda suka yi watsi da yunkurin.

Shugaban ya ce bayan yin nazari akan rikicin da ake faruwa a jihar Rivers, hakan ya sanya ya yi amfani da sashe na 305 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, wajen ayyana dokar tabaci da kuma dakatar da gwamnan da mataimakinsa tare da zabbabbun ’yan majalisar Jihar na tsawon wata shida daga yau Talata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: