Tsohon gwamnan jihar jihar Kaduna Nasiru El – Rufa’i ya zargi gwamnan jihar mai ci Uba Sani, da karkatar da kuɗaɗen ƙananan hukumomin jihar tare da siyan kadarori a ƙasashen Birtaniya, Seychelles da kuma Afirka ta Kudu.

El – Rufa’in dai ya sauye Sheƙa a kwanan nan daga jam’iyya mai mulki ta APC zuwa jam’iyyar SDP, kuma ya yi wannan kalami ne yayin tattaunawarsa da wata kafar yaɗa labarai da ke Kaduna.

Tsohon gwamnan ya kuma yi zargin cewa gwamnan yana canja kuɗaɗen ƙananan hukumomin jihar ne daga Naira Zuwa Dala, tare da siyan kadarori a ƙasashen ƙetare.

El – Rufa’i ya bayyana cewa lokaci da ya ce mulkin jihar bai taɓa ɗaukar ko Naira daga cikin kuɗaɗen ƙananan hukumomin jihar ba, ya na basu kuɗaɗensu ne su yi ayyukansu bayan sun cire kuɗaɗen kula da makarantun firamare da asibitocin sha-ka-tafi da sauran abubuwan da su ka zama wajibi.

Ya kuma ƙara da zargin gwamnatin mai ci da yin almubazzaranci da kuɗaɗen ƙananan hukumomi, amman hukumomi sun zuba ido saboda gwamnan ya na yin hakan ne bisa umarni wasu daga gwamnatin tarayya.

El – Rufa’in ya ce babu wata ƙaramar hukuma a jihar da take karɓara Naira miliyan 50 idan an yi rabon tattalin arziki, su na sace kuɗaɗen ne tare da siyan kadarori a ƙasashen ƙetare.

Ya kuma yi zargin cewa gwamnatin jihar na yin aiki tare da ma’aikatan cibiyar canjin kuɗaɗe, inda su ke taimaka musu wajen karkatar da kuɗaɗen.

Leave a Reply

%d bloggers like this: