Kotun Ƙolin Najeriya ta yanke hukunci ta tabbatar da Samuel Anyanwu a matsayin tabbataccen Sakataren Jam’iyyar PDP na Ƙasa a wani hukunci da kotun ta yanke.

Anyanwu ya kasance na hannun daman Ministan Babban birnin Tarayya Nyesom Wike ne, kuma ya shafe tsawon lokaci na yin takun-saƙa da Sunday Ude-Okoye kan matsayi.

Ude-Okoye dai ya samu goyon baya daga wasu bangarorin jam’iyyar PDP bayan da Kotun daukaka kara da ke Jihar Enugu ta tabbatar da nadinsa, biyo bayan wani hukuncin da babbar Kotun Tarayya da ta yi na tsige Anyanwu.

A hukuncin da kotun ta Koli ta yanke a yau Juma’a mai dauke da kwamitin alkalai biyar karkashin jagoranci mai shari’a Jamilu Tukur, ta ce rikice-rikicen shugabanci a cikin jam’iyya lamari ne na cikin gida, inda kuma hakan ba hurumin kotu ba ne sai dai idan akwai wasu muhimman dalilai.

Kotun ta ce wannan shari’a ka iya shiga hurumin kotu ne matukar ta dangaci karya doka, aikata laifi, ko kuma saɓawa wata yarjejeniya.

Rikicin sakataren Jam’iyyar ta PDP na Kasa dai ya samo asali ne bayan da Anyanwu ya ajiye mukamin Sakataren don yin takarar gwamnan Jihar Imo inda bai samu nasara ba, wanda hakan ya sanya ya yi yunkurin komawa kan muƙaminsa wanda hakan ya haifarwa da jam’iyyar rikici.

Ya yin a kotun daukaka kara ta tabbatar da tsige shi daga kan mukamin nasa tun a watan Disamban 2024, wanda hakan ya sanya Anyanwu shigar da kara gaban Kotun Ƙolin inda ta dawo da shi kan matsayin nasa halastaccen sakataren jam’iyyar ta PDP ta Kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: