Ƙungiyar dattawan arewa Northern Elders Forum ta bayyana damuwarta bisa yadda shugaban Kasa Bola Tinubu ya dakatar da gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara da Mataimakiyarsa da kuma majalisar dokokin Jihar.

Kungiyar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta Farfesa Abubakar Jika ya fita.

Sanarwar ta bukaci da shugaban Kasa Bola Tinubu da ya yi gaggauta dawo da Fubara da Mataimakiyarsa bakin aiki.

Acewar Ƙungiyar duk da cewa sashe na 305 na kundin tsarin mulkin kasa na shekarar 1999 da aka yiwa kwaskwari ya bai’wa shugaban Kasa damar ayyana dokar ta-ɓaci, amma babu wani dalili da zai sanya a ayyana dokar a jihar Rivers a halin yanzu.

Kungiyar ta kara da cewa ya zama wajibi shugaba Tinubu ya samar da hanyar da za a kawo karshen rikice-rikicen siyasa da ake fama da shi a Jihar ta Rivers, tare kuma da janye dakatarwar da ya yiwa Fubara da Mataimakiyarsa da kuma Majalisar dokokin Jihar don ganin an samar da tabbataccen zaman lafiya da kuma tabbatar da dimokuradiyya da adalci.

Sannan kungiyar ta bukaci shugaban da ya sanya idanu sosai domin tabbatar da ganin rikicin da ake samu a wasu jihohin Kasar an magance shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: