Fadar shugaban Kasa ta tabbatar da cewa ko kadan shugaban Najeriya Bola Tinubu ba shi da wata damu akan yadda wasu ke shirin hadewa a Kasar a yayin zaben shekarar 2027 da ke tafe.

Mai magana da yawun shugaban Kasa kan yada Labarai Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan ta cikin wata wallafa da ya fitar, yana mai cewa hadewar manyan ƴan adawar Kasar guri guda ba komai ba ne illa tubalin rashin nasara.

Bayo Onanuga ya ce shugaba Tinubu a halin ya mayar da hankali akan harkokin shugabanci don ganin ya sauke nauyin ‘yan Najeriya.

Acewarsa masu shirin hadewa karkashin inuwa guda ba su da wani buri na kawo ci gaba a Kasa illa burikan kansu.

Bayo na wannan kalami ne bayan wata ganawa da manema labarai da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Alhaji Atiku Abubakar ya yi a birnin tarayya Abuja jiya Alhamis.

Atiku ya bayyana cewa ‘yan adawa sun shirya tsaf domin tunkarar shugaba Tinubu a 2027, bayan yin wani taro karo na farko da ‘yan adawa suka yi a Kasar kan batun dunkulewarsu guri guda.

Daga cikin wadanda suka halarci taron sun hada tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party Peter Obi, wanda Yunusa Tanko ya wakilta, sai tsohon sakataren gwamnatin Tarayya Babachir Lawal, da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Elrufai, Sakataren Gamayyar Jam’iyyun Siyasa na Ƙasa CUPP Peter Ameh da dai sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: